A tattaunawar da aka fara a Washington, Jami’an kasar Mexico sunce tattaunawar su da shugaba Trump akwai adadin inda zasu kai domin karrama bukutar shi ta hana kwararar bakin haure shiga Amurka ta kasar Mexico domin kaucewa Karin haraji na kashi biyar a mako mai zuwa.
Jami'an sun kara wata doka a yarjejeniyar dake bukata duk wani mai neman mafaka a Amurka da farko sai ya fara neman mafaka a Mexico tukunna.
“akwai adadin da zamu iya kaiwa mu amince a yarjejeniya, adadin kuwa shine martabar Mexico, a cewar jakadan Mexico a Amurka Martha Barcena.
Bercena ta kara da cewa harajin Amurka, zai iya haifar da matsalar tattalin arziki da rashin daidaito, wanda zai hana Mexico daukar mataki kan dakatar da kwararar bakin haure da suke shigowa daga Guatemala,Honduras, El Salvador.