Wata kwallo da Lionel Messi ya jefa a ragar PSG a daren jiya Laraba, inda kwallan ta kawo shi dai dai da shahararren dan wasan Real Madrid Raul, a cikin ‘yan wasan da suka fi cin kwallaye a gasannin Turai.
Dama tuni Messi ya wuce Raul a yawan kwallaye da ya jefa a gasar Champions, amma yanzu jimlar adadin kwallaye da Messi ya jefa a gasannin Turai yayi kunnen doki da na tsohon dan wasan kasar Spain wato Raul Gonzalez.
Lionel Messi ya jefawa Barcelona kwallon farko cikin minti goma sha tara da fara wasa, kwallon daya jefa ta kawo shi kunnen doki da fitatcen tsohon dan wasan kungiyar Real Madrid Ra’ul, a littafin tarihi na wanda sukafi kowa jefa kwallaye a gasar wasan turai.
Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo shine yazo na biyu da jefa kwallaye 75, shi kuma tsohon dan wasan AC Milan Filippo Inzaghi yazo na uku da kwallaye guda 70 a raga.
Sunayen ‘Yan Kwallon Kafa Da Suka fi Kowa Cin kwallaye A Gasar Turai.
Dan Wasa |
Yawan Kwallaye |
Lionel Messi, Raul |
76 |
Cristiano Ronaldo |
75 |
Filippo Inzaghi |
70 |
Gerd Muller |
69 |
Andriy Shevchenko |
67 |
Your browser doesn’t support HTML5