Hukumar kwallon kafar Najeriya wato (NFF), tayi alkawarin bada cikakkiyar goyon baya ga kungiyar mata ta Super Falcons, alokacin da suke fara shirye shiryen gasar mata na cin kofin duniya na hukumar kwallon kafa ta FIFA da zata gabatar kasar Kanada.
Najeriya dai na daga cikin rukunin da kasar Sweden, Amurka, da Australia. Shugaban hukumar NFF ya tabbatar da cewa akwai matukar aiki ga samun wuce wannan rukunin da Najeriya ta samu kanta ciki, amma yayi alkawarin cewa za’a samar wa da zakarun Afirkar duk abun dasuke bukata wajen shiri.
Yakuma kara da cewa alkawarin da mukayiwa kungiyar Super Falcons na tabbatar da ganin mun basu shirin da suke bukata, za’a kaisu guri mai kyau a inda zasu sami horo na karshe, kuma zasuke buga wasannin kawance masu ma’ana kafin zuwa wasanin karshe.
Yana da kyau ace munyi kwazo sosai harma yawuce wanda mukayi abaya, kamar yadda muka mamaye nahiyar Afirka haka muke so mu fara mamaye duniya baki daya.
Kuma muna da ‘yan wasa da zasu iya fitowa a ko ina cikin ‘yan wasan duniya, kamar yadda aka gani a gasar mata ta ‘yan ‘kasa da shekaru ashirin (U-20) da akayi a kasar Kanadar a watan Agusta na wannan shekarar.
Abunda kungiyar take bukata shine karawa da fitattun kungiyoyin wasanni kwallon kafa na duniya da zai basu dama game da daukar dabaru da shirye shiryen horaswa.
Najeriyar dai zata kara da kasar Sweeden a wasan farko na gasar a takwas ga watan yuni a kasar Kanada.