Tun a shekarar bara ne dai ake alakanta Griezmann da komawa Barcelona, haka ma a bana bayan da ya bayyana aniyarsa ta barin kungiyarsa a bana.
A shekara 2018 Griezmann ya yi watsi da tayin da Barcelona ta masa inda kungiyar sa ta Atletico Madrid ta zargi Barcelona da zawarcin dan wasan dan kasar Faransa ta hanyar da ba ta dace ba.
Messi ya ce a maimakon sayen Griezmann, kamata ya yi Barcelonan ta maido da tsohon dan wasanta Neymar, wanda ta sayar wa kungiyar PSG kan zunzurutun kudi har euro miliyan 198 a shekarar 2017.
Barcelona ta yi fafutukar ganin ta saye dan wasan da zai maye gurbinsa, a kokarin hakan ne, kungiyar ta sayi Philippe Coutinho daga Liverpool da kuma Ousmane Dembele daga Borussia Dortmund.
Sai dai har yanzu 'yan wasan biyu, sun gaza nuna kwazo kamar yadda ake tsammani.