“Kowanne daga cikinmu ya fito ne daga kasar dake da irin nata kalubalen,” a cewar Melania lokacin da take magana gaban wani taro a gefen babban taron shugabannin kasashe na MDD, ta ci gaba da cewa “amma na sani a zuciyata baki dayan muna da kudurin rainon manyan gobe su zama suna cikin farin ciki, da lafiya har zuwa girmansu.”
Fadar shugaban Amurka ta White House ta ce Melania za ta kai ziyara ne kasar Ghana da Malawi da Kenya da kuma Masar.
Hukumar raya kasashe ta Amurka USAID ce zata taimaka mata wajen shirya wannan tafiya, haka kuma a wannan ziyara ta ta zata mayar da hankali ne kan lafiyar iyaye mata da jariransu, abinci mai gina jiki ga mata da yara kanana, ilimin kananan yara da kare namun daji da kariya ga cuta mai karya garkuwar jiki.
Haka kuma ana sa ran Melania za ta bayyana rawar da Amurka ke takawa wajen taimakawa kasashen da zata ziyarta.