Shugaba Nana Akufo Addo ya jaddada muhimmancin ganin an baiwa nahiyar Afirka wakilci na din din a kwamitin na sulhu. Ganin kashi 50 cikin dari na ayyukan kwamitin duka a nahiyar ta Afirka aka gudanar su, walau kiyaye zaman lafiya ko ayyukan jinkai.
Shugaban yace shugabbin Afirka sun gaji da yawo da kokon bara a hanau suna neman tallafi a duniya. Yace burin shugabannin shine samun kawaye shigen yadda nahiyar take yi yau da China, domin shugabannin su gina kasashe da za su wadaci al'umar su da ayyukan yi da kuma kayan more rayuwa.
Shugaba Addo, yace akwai bukatar majalisar ta kau daga zama mai tsara kudurori ba tareda an sami aiwatar da su ba. Yace akwai bukatar shugabannin majalisar a yau su tashi haikan su magance matsalolin da suka addabi duniya a yau, shigen aikin da magabatan da suka yi a lokcinda aka kafa wannan majalisa shekaru.
Ga karin bayani a rahoton da Baba Yakubu Makeri
Facebook Forum