Aliyu Shehu Yakasai – tsohon ma’aikacin gidan talabijin na NTA, sannan wani jigo a masana'antar Kannywood wanda ya ga jiya ya ke ganin yau, kwararren a fannin Production Design wato mai tsara shiri tun daga farkon har zuwa karshe.
Wanda aka fi sani da Baba Ali, ya shafe shekaru da dama da fara harka ta fim a cewarsa, sai da aka fara fina-finan Hausa kafin 'yan kudu suka fara harka ta fim, dalilin da ya sa 'yan kudu suka yiwa masana’antar Kannywood nisa shine sun fi mai da hankali.
Yawan kura-kuran da ake samu a fim, shine ko da sun yi yunkurin ba da shawara sai wadanda suka zuba kudinsu domin fitar da fim su ce ai kudinsu ne, ko kuwa su ce ma wanda yayi musu gyara da cewar ai kudinsa ne, don haka zai yi abinda ya ga dama.
Baba Ali, ya kara da cewa akwai kungiyoyi a Kannywood din, amma ba’a bin dokokinta, sannan mafi akasarin wadanda ke harkar fim a yanzu suna da karanci yadda harka ta ke, dole kuwa a samu kura-kurai.
Dangane da yadda ake sanya rawa a fina-finai, sai yace ba laifi ba ne don a sa rawa a fim amma babban abin la’akari shine ko an bi turban da ya dace, ko akasin haka.
Your browser doesn’t support HTML5