WASHINGTON D.C —
Yayin da ake ci gaba da fama da karancin man fetur a wasu jihohin arewacin Najeriya, matasa da dama na cin karen su ba babbaka wajan sana'r bumburutu, shin ya dace matasa su raja'a wajan wannan sana'ar da suke nunka farashin man fetur daga yadda suka saye shi?
Muna bukatar sakonnin maza da mata akan wannan tambaya, kuma za’a iya aiko mana da sakon ta murya a kafar sada zumunta ta WhatsApp mai lamba +12025775834. Kada a manta a fadi suna da kuma jiha ko gari.
Ana iya sauraren wannan shiri a duk lokacin da ake bukata a shafinmu mai adireshi www.dandalinvoa.com