A Shirin mu na samartaka, yau mun tattauna ne da wasu matasa mata da maza inda suka amsa tambayar mu ta wannan makon, shin menene yafi burge ku, ko ci maku tuwo a kwarya a harkokin soyayya?.
matasan sun bayyana ra'ayoyin su kamar yadda kowanne ya fahimci rayuwa da zamantakewa da kuma yau da kullum.
Koda shike ra'ayoyin sun banbanta, kamar yadda wasu 'yan mata suka bayyana karara cewar abinda ya fi bata masu rai shine ganin suna tare da saurayin su kuma yana amsa kiran waya daga wata yarinya, ko kuma suna tafiya akan hanya suka wasu 'yan mata na kallon shi.
Samari fa?, Da dama sun bayyana nasu ra'ayoyin wadanda yawanci suna kama da na 'yan matan ne sai dai kowa nada inda ya fi masa ciwo, misali yawancin samari sunfi korafi ne akan yadda wasu samari ke nuna kudi ko abin duniya domin raba su da 'yan matan da suke kauna.
Ku same mu a shafinmu na dandalinvoa/facebook.com domin tafka muhawara.
Ku saurari ra'ayoyin wasu samari da 'yan matan da muka tattauna da su