Kocin kungiyar kwallon Kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, na shirin sayen dan wasan tsakiya na Chelsea, Eden Hazard, mai shekaru 27 da haihuwa akan kudi fam miliyan 100.
Kocin kungiyar kwallon Kafa ta Chelsea, Antonio Conte, na shirin barin matsayin sa a kungiyar nan da awoyi 48, inda aka sanya sunan tsohon Kocin Barcelona, Luis Enrique, a cikin jerin wadanda ake ganin zasu maye gurbin Conte a kungiyar.
Manchester United, ta cimma wata yarjejeniya na wucin gadi tsakanita da kungiyar kwallon Kafa ta Benfica, kan dan wasan tsakiyarta mai suna Talisca, wanda yanzu haka yake zaman aro a kungiyar Besiktas.
Kocin Manchester United Jose Mourinho, ya rufe shafinsa na sada zumunci Instagram, sakamakon sakonnin da ake turo masa kan zarginsa da ake yi na rashin samun nasara da Manchester united, bata yi ba a wasan karshe na cin kofin kalu bale (FA Cup) 2017/18 tsakaninta da Chelsea. ranar asabar da ta gabata 19/5/2018, inda aka doke Manchester united da kwallo1- 0.
Saurari cikakken labarin a nan.
Your browser doesn’t support HTML5