Me Ya Sa Shekarau Ya Yada PDP?

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahin Shekarau (Hoto: Shafinsa Na Twitter)

Wannan dai wani sabon babi ne da aka bude a takaddamar da ake yi tsakanin Shekarau da abokin hamayyarsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya koma jam’iyyar ta PDP a watan Yuli.

Rohatanni daga Najeriya na cewa, tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga jam’iyyar PDP.

A iya cewa wannan ya yi daidai da karin maganar nan na Hausawa da ya ce “karshen tika tika tik?”

Wannan dai wani sabon babi ne da aka bude a takaddamar da ake yi tsakanin Shekarau da abokin hamayyarsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya koma jam’iyyar ta PDP a watan Yuli.

Shekarau ya ce ya dauki matakin ne saboda rashin adalci da aka nuna masu.

“Kwamitin rikon kwarya da aka nada (caretaker) gaba daya an dauka an mikawa wasu, ka ga nan babu adalci, daga cikin mutum bakwai, mutum biyar daga bangare daya suka fito.”Inji mai ba Shekarau shawara kan harkokin yada labarai, Sule Ya’u Sule, a wata hira da ya yi da wakilin Muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari.

Reshen jam’iyyar ta PDP a Kano ya shiga rudani ne tun bayan da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya koma jam’iyyar ta PDP.

Da ma masana kan harkokin siyasa, sun yi hasashen za a iya samun rashin jituwa tsakanin Kwankwaso da Shekarau, wanda shi ke rike da jagorancin jam’iyyar ta PDP a jihar ta Kano gabanin komawar Kwankwaso.

An yi ta kai ruwa rana kan raben mukamai a jam’iyyar ta PDP tsakanin Shekarau da Kwankwaso, lamarin da ya sa hedkwatar jam’iyyar ta shiga tsakani.

Sai dai irin matakan da hedkwatan ke dauka na sasanta rikicin, kamar yadda bayanai ke nunawa, ba su yi wa Shekarau dadi ba, domin akwai alamu, hedkwatar na goyon bayan Kwankwaso ne kamar yadda bangaren su Shekarau suka lura.

Da ma dai shi Shekarau asalin dan jam’iyyar APC ne, hasali ma da su aka kafa ta.

Amma duk da haka, Sule ya ce, ba zai yi wu Shekarau ya ci gaba da kasancewa a PDPn ba, yana zargin cewa hedkwatar jam’iyyar ta fito karara tana goyon bayan Kwankwaso.

Al’amura sun sake dagulewa ne tun bayan da aka nada Rabiu Suleman Bichi a matsayin shugaban kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar ta PDP a Kano.

Bichi ya kasance na hannun daman Kwankwaso.

Baya ga haka, kwamitin wanda ke dauke da mambobi bakwai, ya hada da makusantan Kwankwaso biyar, yayin da mambobi biyu kacal aka ba bangaren su Shekarau da Aminu Wali.

Kafa kwamitin rikon kwaryar, ya biyo bayan rushe majalisar zartarwar jam’iyyar da hedkwatar jam’iyyar ta PDP ta yi a karshen makon da ya gabata sanadiyar rikicin.

Masu lura da a’lamura sun ce matakin rushewar, kofa ce aka budewa Kwankwaso ya karbi ragamara jam’iyyar ta PDP a Kano.

Da ma dai shi Kwankwaso asalin dan jam’iyyar PDP ne kafin ya koma APC.

Hakan wasu ya sa ke kwatanta wannan lamari a matsayin “idan mai wuri ya zo, sai mai taburma ya nade.”

Jaridar yanar gizo ta Daily Nigeria, ta ruwaito cewa, mataimakin shugaban Najeriya, Prof. Yemi Osibanjo ne ya ya yi amfani da wannan rudanin siyasar jihar ta Kano ya yi zawarcin Shekarau kan ya koma APC, tare da yi masa wasu alkawura.

Daga cikin alkawuran da aka yi wa Shekarau a cewar jaridar ta Daily Nigeria, akwai batun cewa za a ba shi mukamin Minista.

Jaridar ta yanar gizo ta ce, Shekarau zai ayyana shirin ficewar shi daga jam'iyyar ta PDP a yau Talata.

Tuni dai har gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya gana da Shekarau, kamar yadda jaridar ta bayyana.

A ‘yan watannin bayan nan, gaggan ‘yan siyasa a Najeriya sun yi ta sauya sheka a tsakanin manyan jam’iyyun siyasar kasar.

Wane tasiri wannan sauya sheka ta Shekarau za ta yi ga siyasar Kano da Najeriya? Ya ya zaben 2019 zai kasance? Wacce jam’iyya ce za ta lashe zaben 2019 a jihar ta Kano?

Wadannan tambayoyi ne da lokaci ne kadai zai iya bayyana amsoshinsu.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

Me Ya Sa Shekarau Ya Yada PDP? '2:32"