Me Ke Sa Wasu Samari Bin Tsofaffin Mata?

Kamar yadda Dandalin voa ya zanta da wasu 'yan mata wadanda suka bayyana ra'ayoyin su akan dalilanda yasa suke yarda da wasu maza sa'o in iyayen su, yau kuma mun ji ta bakin samari ne.

Idan mai karatu bai manta ba, yawancin maza matasa na da ra'ayin nuna wa 'yan mata isa, ko wadata. Haka ma wasu matan musamman wadanda suka manyanta, wasu kan yi anfani da dukiyar da suka mallaka domin jan hankalin wasu samari.

A tattaunawar mu da wasu samari, sun fito karara sun bayyana cewar lallai suna da mata wadanda sun manyanta amma basu sami yin aure ba, ko kuma sun taba yin auren amma sun fito kuma suna da abin hannu dan haka sukan rufe ido su rika nuna masu soyayya amma ba domin su aure su ba.

Yawancin samarin sun bayyana cewa sukan amshi kudade daga wurin matan amma daga karshe sai su ba 'yan matan su ba tare da sun nuna masu inda suke samo kudin ba.

Koda shike ba'a taru an zama daya ba, wasu kam irin nasu ra'ayin daban yake..

Saurari cikakkiyar hirar a dandalinvoa.com