MDD Za Ta Taimakawa Nahiyar Afrika

Sakatare Janar Na MDD Antonio Guterres

Babban Sakataran Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce an samu gagarumin ci gaba a dangantakar da ke tsakanin Majalisar ta Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar Afirka ta AU.

Inda ya yi fatan hakan zai taimaka wajen shawo kan matsalolin da ke addabar nahiyar.

Guterres ya ce, Burinmu shi ne, mu taimakawa nahiyar Afirka ta shawo kan matsalolinta, ta yadda za a daina yiwa nahiyar kallon mai cike da dumbin matsaloli.

Sannan ya kuma yi nuni da yadda aka shawo kan rikicin Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Yayin da kungiyoyi masu dauke da makamai, suka cimma wata matsaya a Sudan, kan kawo karshen rikicin kasar, wanda aka kwashe shekaru biyar ana yi.