MDD Za Ta Maida Hankali Akan Ilimi Da Inganta Rayuwar Mata

Babban taron MDD na 73

A karo na hudu cikin shekaru 73 da aka fara baban taron Majalisar Dinkin Duniya, an zabi mace ta yi jagoranci lamarin dake nuni da cewa taron duniyan zai mai da hankali ne akan mata, ‘yan mata da matasa

Babban taron Majalisar Dinkin Duniya, MDD da aka bude tun ranar 18 ga wannan watan na Satumba, yanzu ya kai wani matsayi mai mahimmanci a yau Talata 25 ga wannan wata.

Shugabannin kasashen duniya da suka hada da shugaban Amurka Donald Trump sun fara gabatar da jawabai yayinda ake ci gaba da tarukan ministoci da wakilan kasashen duniya a gefe guda.

Wannan babban taro dake tattaro shugabannin duniya y aba da mahimmanci akan batutuwan da suka shafi mata da kyautata rayuwarsu

Zabar Maria Escavosa Garsis a matsayin shugabar taron na wannan shekarar da ya kasance na 73, ita ce mace ta hudu da za ta taba zama shugabar taron kamar yadda tarihi ya nuna. Kazalika wani yunkuri ne na jaddada yin kira game da maida hankali akan yaki da tsangwamar mata da kuma karfafa musu gwiwa a cikin harkokin siyasa a duk wasu jawabai da za’a yi a taron.

A wannan babban taron na MDD an shirya tattauna batutuwa dake da mahimmanci akan harkokin mata, kama daga kawo karshen cin zarafin mata da ‘yan mata da kuma daidaiton daukan albashi, da shirye shiyen agazawa mata bakin haure dai sauransu.

Loretta Anocie mataimakiya ta musamman ga shugaban Nigeria akan harkokin kafafen yada labaru ta bayyana abun da za’a gabatar a taron da aka shiryawa mata.

Ta ce “ za mu gabatar da batun da ya shafi mata da Kananan yaran Afirka saboda muna da matsaloli iri daya kuma al’adu iri daya. Bayan haka matan shugabannin Afirka za su tattauna akan wannan batu ta yadda za’a taimakawa kasashen Afirka.

Ta ci gaba da cewa “tattaunawar matan shugabanin kasashen zai kuma maida hankali akan mata da matasa, musamman ilimin yara mata”.

Wannan taron matan zai kuma tattauna akan yaki da cutar kanjamau kamar yadda Mrs. Bassey, daya daga cikin tawagar matan Nigeria ta bayyana. “Kungiyar matan shugabannin kasashen Afirka dake yaki da cutar kanjamau za ta yi taronta, ana kuma sa ran duk matan shugabannin Afirka za su halarci wannan taron”.

Tuni dai shugabannin kasashen duniya suka fara jawabansu yayinda ake kyautata zaton shugaban Nigeria Muhammad Buhari shi ma zai yi nashi yau.

A saurari rahoton Baba Yakubu Makeri

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Mata A MDD Zai Maida Hankali Akan Ilimi Da Inganta Rayuwar Mata – 2’ 55”