WASHINGTON DC - Kudirin wanda ya samu goyan bayan kasashe 14, ya bukaci tsagaita wuta a gaza nan take albarkacin watan ramadan mai tsarki tare da sakin ilahrin mutanen da hamas ke garkuwa dasu.
Hawa kujerar nakin wani gagarumin sauyin manufa ne daga bangaren Amurka, wacce ke amfani da matsayarta ta me kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wajen hawa kujerar naki a kudirori 3 da aka zartar a baya na neman tsagaita wuta a gaza.
Matakin ya biyo bayan karuwar matsin lambar da gwamnatin Shugaba Joe Biden ke fuskanta daga cikin jam'iyyarsa, dama kawayen Amurka na kasa da kasa, akan cewa dole Amurka ta kara yin matsin lamba akan isra'ila ta takaita hare-haren da take kaiwa gaza, a daidai lokacin da adadin wadanda suka mutu a zirin ya zarta mutum dubu 32 kuma fiye da mutane milyan guda ke daf da fadawa cikin ja'ibar yunwa.
A baya Amurka tayi karan tsaye ga kudirorin Majalisar Dinkin Duniya dake neman tsagaita wuta nan take har sai 3, harma da wanda gamayyar kasashen Larabawa suka gabatar a watan daya gabata, inda ta kasance kasa daya tilo daga cikin mambobin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya 15 data hau kujerar naki.
Tun daga shekarar 1945, ta hau kujerar naki akan kudirorin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya har sau 89- kuma fiye da rabin adadin kudirori ne da suka sabawa muradan Isra'ila.