Wani babban jami’in diplomasiyyar kasar Syria, ya yi kira ga dakarun Amurka da na Turkiyya da su yi gaggawan ficewa daga kasar, yana mai cewa gwamnati na da ‘yancin da za ta kare iyakokinta ta kowace irin hanya, muddin suka ci gaba da zama a kasar.
A jiya Asabar Ministan harkokin wajen Syria, Walid Al Moallem, ya gabatar da wannan korafi a zauren Majalisar Dinkin Duniya, yayin da ake shirin nade taburmar babban taron na shekara-shekara.
Kiran na zuwa ne yayin da Amurkan da Turkiyya ke kokarin cimma wata matsaya a tsakaninsu, ta samar da yankin da za a mayar da shi “tudun mun tsira” a tsakanin kan iyakokin Turkiyyar da Syria.
Mouallem ya kuma jaddada goyon bayan gwamnatin kasar kan sabon kundin tsarin mulkin da za a samar.
Yakin basasar kasar ta Syria, ya faro ne tun daga shekarar 2011 a lokacin guguwar sauyi da ta ratsa kasashen larabawa, abin da ya yi sanadin mutuwar mutum dubu 400 kana wasu miliyoyi suka tsere daga kasar ta Syria.