Taron, wanda Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta zai tara gwamnatocin, da kungiyoyin bada agaji, da wasu kungiyoyi na al’umma don tattauna yadda za ‘a sami taimakon gaggawa ga ‘yan Siriya kusan miliyan 5 da suka tsere zuwa kasashen Jordan, Lebanon, Turkiyya, da wasu wuraren. Haka kuma, za a nemi kirkiro da wata dabara ta dogon lokaci, ta taimaka musu wajen farfado da rayuwarsu, ciki har da ilimi, da ayyukan yi. Dubun dubatar ‘yan Siriya sun kwarara zuwa kasashen turai don neman mafaka, abinda ya zamo rikicin gudun hijira mafi girma da aka taba gani tun bayan yakin duniya na biyu.
Bayan haka Majalisar Dinkin Duniya na neman karin dala miliyan dubu 1 da dari 2 don taimakawa kasashen da yakin ya shafa don su samu su fito da hanyoyin da za su taimakawa dumbin ‘yan gudun hijirar.
Firayin ministan Britaniyya David Cameron ya fadi cewa wanna taimakon zai ba ‘yan siriya kwarin guywar da su ke bukata don su kawar da duk wani tunanin cewa don basu da mafita ne shi ya sa su ka jefa rayukansu cikn hadarin zuwa kasashen turai. Gabanin taron, Mr. Cameron ya sanar da cewa Britaniyya za ta bada gudunmuwar dala miliyan dubu 1 da 750.