Mazauna Yamai Na Zargin Tashar Samar Da Wutar Lantarki Da Gurbata Yanayi Da Mahalli

Wadansu mazauna birnin Yamai sun koka game da abinda suka kira barazanar da suke fuskanta daga wata sabuwar tashar samar da wutar lantarki mai karfin Megawatt sama da 80 da aka kafa a tsakar gari ba tare da la’akari da ka’idodin da doka ta shimfida ba.

Sama da wata 1 bayan kaddamar da ayyukan tashar samar da wutar lantarkin da kamfanin Nigelec ya baiwa wani kamfanin kasar Mauritania kwangilar gudanarwa, mazauna unguwanin da suka hada da Koira, Kano, Goudel, Sonuci, Koubia, Yantala da Bobiel sun fara kokawa a game da mawuyacin halin da suka tsinci kansu.

Sun kuma kara da cewa samun barci ya yi wuya sakamakon karan injina yayinda aka fara ganin alamun gurbacewar iskar da ake shaka a irin wadanan unguwani kamar yadda suka bayyana a wata sanarwar da suka fitar.

Zancen nan da ake wasu daga cikin irin wadanan mutane sun fara jin wasu alamomi masu kama da na kamuwa da wata rashin lafiya sakamakon gurbacewar yanayi injisu.

Gwamman mutanen da suka hadu a wannan gangami don kalubalantar tashar ta Centrale Nigelec Goudelsun bukaci hukumomin kolin kasa su dubi wannan matsala tun wuri bai kure ba.

A wata wasikar da ya aikewa kungiyar kare hakkin masaya ta CODDAE a makon jiya darektan kamfanin Nigelec Kalid Alassan ya yi watsi da dukkan matsalolin da kungiyar ta yi zargin tashar ta haddasa domin a cewarsa an kafa ta ne tare da mutunta dukkan ka’idodin da ya kamata.

Saurari cikakken rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Mazauna Yamai Na Zargin Tashar Samarda Wutar Lantarki Da Gurbata Yanayi Da Mahalli