Mazauna jihar Florida sun bi kan tituna inda ruwan da yayi ambaliya yake kwance don tatara tarkace da kuma duba irin baranar da tayi a gidajensu, bayan da guguwar Hurricane Milton wanda ta ratsa ranar Jumma’a a wuraren da ke gabar teku gabanin ta rikide zuwa mumunar Tornadoes.
Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ta bada rahoton cewa, akalla mutane 10 ne suka mutu, sannan masu aikin ceto suna ci gaba da ceto wadanda suke raye, amma mutane da dama sun bayyana farin ciki cewa Milton bata yi muni sossai ba. Yankin Tampa dake da karancin mutane, sun tsallaka rijiya da baya yayin da guguwar take kadawa, lamarin da masana kimiyya sukayi fargabar irin barnar da sukayi tsammani zata yi a nan.
Gwamna Ron DeSantis ya yiwa mutane gargadi da su kiyaye, sannan kuma yayi bayani a kan irin barazanar kariyar dake tattare da turakun wuta da shiga cikin ruwa inda zai iya kasancewa akwai abubuwa masu hatsari suna yawo a ciki.
“Yanzu lokaci ne da mutane zasu iya mutuwar da za a iya hana faruwar sa,” abinda DeSantis ya fada Kenan. Ya kuma kara da cewa, “Ya kamata ku dau matakan da suka dace sannan ku sani cewa akwai abubuwan dake tattare da hadari anan.”
Ya zuwa daren Jumma’a, alkaluman mutanen da basu da wutar lantarki ya ragu zuwa mutum miliyan 1.9, bisa bayanan poweroutage.us, wani shirin dake bibiyar mutanen da basu da lantarki a Amurka.
An sanar da mutane dubu 260,000 mazauna birnin St. Petersburg cewa, su tafasa ruwa kafin su sha, ko suyi amfani da shi wajen girki ko wanke bakin su , har sai zuwa akalla ranar Litinin.