A gobe asabar ne dai za’a gudanar da damben boxing tsakanin tsakanin kwararren ‘yan danben nan biyu Floyd Mayweather ‘dan Amurka da Manny Pacquiao ‘dan asalin kasar Philippines.
Floyd Mayweather dai ya bayyana kwarin gwiwar cewa shi ne zai yi nasara damben da za’ayi gobe Asabar, da kowa ke jira ya gani.
Ana tsammanin idan har Kwararren ‘dan damben na Amurka ya sami nasara a wannan danban da za’a yi, to zai iya samun kudi kimanin yiro miliyan ‘dari €100million. ‘Dan damban na kuma ganin ya cancanci duk wani kwabon da ke cikin kudin, ya kuma ce ba zai bai wa mutane kunya ba.
Mayweather da Pacquiao za su shiga filin dambe ranar Asabar a birnin Las Vegas da ke jihar Nevada ta Amurka, ‘Dan wasan danben dai yace, “ban san wani abu ba banda nasara, bani da wata shakka cewa zan yi galaba.”
Ya cigaba da cewa mutane nata magana kan fafatawar, na shirya in shiga fagen daga nayi abinda na saba yi ranar biyu ga watan Mayu.
Mayweather, ‘dan shekaru 38 da haihuwa, ya kuma fadi yadda zai kashe kudinsa idan har ya sami nasarar a wasan. Inda ya bayyana cewa, “zan cigaba da gudanar da rayuwata, na kuma taimakawa iyalina dama mutanen dake kusa dani, hakan shine zai sa naji dadi.
Danben Boxing sana’a ce wadda mutane basu san ta yadda ake kwarewa akai ba, amma ni kam hankali na a kwance ya ke. Sansanin horon nada kyau kuma na shirya yin wannan damben a daren da za a yi”