An dai shirya ficewa Birtaniya a ranar 29 ga watan Maris, amma May ta samu amincewar daga tarayyar Turai na dan wani karamin karin lokaci da zai bai wa gwamnatin dama ta samu mafita da 'yan majalisar kasar za su amince.
WASHINGTON D.C. —
Firai Ministar Burtaniya, Theresa May, ta ce za ta kara neman a jinkirta shirin ficewar kasar daga kungiyar tarayyar turai, domin a bai wa majalisar dokokin kasar, isasshen lokacin da za ta amince da tsarin da kasar za ta bi, wajen janyewa daga kungiyar ta EU.
Ya zuwa yanzu, sau uku majalisar tana watsi da tsarin da May ta gabatar, bayan shekaru biyu da aka kwashe ana tattaunawa da kungiyar ta tarayyar turai.
May ta ce, tana kokarin ganawa da shugaban babbar jam’iyyar adawa ta Labour, Jeremy Corbyn, domin su cimma matsaya kan wani tsari na ficewa daga kungiyar ta tarayyar turai, wanda ‘yan majalisar za su amince da shi.