Kimanin mutum 20 ne suka mutu a jamhuriyar Nijar, sakamakon wata turereniya da aka yi a garin Diffa, a lokacin da ake shirin rabon wani tallafi da gwamnan jihar Borno ya bayar domin ‘yan gudun hijirar Najeriya da suka tserewa rikicin Boko Haram.
Lamarin ya wakana ne da sanyin safiyar yau Litinin 17 ga watan Fabarairu, a filin wasanni na birnin Diffa wato MJC. Inda dimbin mutane maza da mata suka yi asubanci don zuwa karbar tallafin, a cewar shaidun gani da ido lokacin zantawa da manema labarai.
Kawo yanzu, rahotanni sun tabbatar da mutuwar kimanin mutum 20, galibin su mata da yara kanana, wasu da dama kuma sun ji rauni sanadiyar wannan turereniyar.
Mara Mamadou shine shugaban kungiyar Alternative Espace Citoyen a yankin Diffa, ya ce tun da misalin karfe 5 mutane da suka ji labarin taimakon da aka bayar, sai suka cika kofar wurin rabon kayan tallafi, dalilin da yasa, da safe koda aka bude kofa, sai aka tattake wadanda ke nan, inda mata da yara guda 20 suka rasa ransu.
Gwamnan jihar Diffa Issa Lemine dake jagorancin wata tawagar jami’an hukumar jihar, sun ziyarci wurin da wannan al’amari ya faru kafin su leka asibitocin, da aka ajiye gawarwakin mutanen da suka rasu.
Koda yake ba wani jami’in hukumar lafiya da ya yi tsokaci akan batun, wani hakimi da bai so a bayyana sunansa ba ya ja hankalin jama’a, ya ce neman abun duniya ne ya kawo haka, abinda ya fi shine, kowa yayi hakuri da kadan, mai rabo baya rasa samu.
A rabon da Gwamna Umaru Zulum ya jagoranta a jiya Lahadi, kowanne dan gudun hijira ya sami kusan naira 5,000 hade da kayan abinci kamar shinkafa, man girki da suga, abinda ya kwadaitar da ‘yan gudun hijirar har ma da wasu ‘yan gari suka yi asubanci zuwa wurin da ake shirin ci gaba da rabon wannan tallafi a yau Litinin, dalilin wannan turereniya kenan.
‘Yan Najeriya akalla 12,0000 ne suka yi hijira zuwa yankin Diffa shekaru kusan 7 kenan, sanadiyar rikicin ‘yan kungiyar Boko Haram yayin da wasu dubban ‘yan Nijar suka yi kaura daga garuruwansu saboda tabarbarewar al’amuran tsaro.
A saurari rahoto cikin sauti daga birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar.
Your browser doesn’t support HTML5