Mawakiya Jemiriye Ta Samu Karbuwa A Kasashen Duniya

Mawakiya Jemiriye

Wakokin Jemiriye sun samu karbuwa sosai ba a Legas kadai ba har ma da kasashen duniya.

Labarin mawakiya Jemiriye Adeniji na da matukar ban sha'awa, saboda yadda wakokinta suka kunshi al'adun gargajiya na Afirka da ma na zamani kuma suna bayyana tushenta.

Jemiriye 'yar asalin Najeriya ce, amma tana zama a garin Pittsburgh da ke jihar Pennsylvania a Amurka.

Bayan haka wakokinta sun kunshi labarin abubuwan rayuwarta da ƙalubalen da ta fuskanta ko take fuskanta, da kuma nasarorin da ta cimma.

Yanayin muryar Jemiriye na jan masu sauraro zuwa duniyarta ta musamman, inda take bayyana masu burinta.

Jemiriye ta yi fice wajen jajircewa kan harkokin zamantakewa, musamman karfafa wa mata matasa gwiwa a fannin ilimi da fasaha, inda ta yi imanin cewa waka na da karfin da zata iya kawo kyakyawan sauyi.