An saki fim din ne a ranar Juma’a, wanda yake dauke da fitaccen jarumin Hollywood Eddie Murphy.
“Wannan babban abin farin ciki ne a ce na fito a fim da wasu daga cikin mutanen da suka sa ni dariya a lokacin ina yaro.” Davido ya wallafa a shafinsa na Instagram hade da wani hoton bidiyo da ya nuna mawakin yana kallo a talbijin.
Davido dai ya fito ne a wani wajen biki inda ya rera wakar “Assurance,” a dandamalin taron.
Coming To America na farko, fim ne da Eddie Murphy ya fito a matsayin yarima Akeem Joffer tare da abokinsa Semmi (Arsenio Hall) wadanda suka yi balaguro daga masarautar Zamunda da aka kikira a fim din zuwa unguwar Queens da ke birnin New York a Amurka a shekarun 1988.
A fim din, Akeem ya samo matar aure daga Amurka Lisa ( Shari Headley) wacce ya tafi da ita Zamunda aka daura musu aure.
A wannan fim din, bayan shekara 30, Akeem ya saka nikar gari don zuwa Amurka – a wannan karon don neman dansa Lavelle (Jermaine Fowler.)
Shi dai wannan fim wanda masoyan Eddie Murphy suka yi ta jira ya fito, ya tattaro kusan daukacin wadanda suka fito a na farko hade da wasu fitattun jaruman Hollywood da mawaka.
Fim din wanda Craig Brewer ya ba da umurni ya hada har da juramai irinsu Wesley Snipes, Lesley Jones da Tracy Morgan.
Har ila yau a cikin fim din, an saka wakar Tiwa Savage wacce ita ma fitacciyar mawakiya ce daga Najeriya.
Baya ga ita, akwai wasu mawakan daga nahiyar Afirka da su ma aka saka wakokinsu a fim din.