Samaila Bahago, wanda aka fi sani da 'Slim B' mawakin nanaye, da sauransu wanda ya ce waka wata hanya ce da ake isar da sakoni cikin sauki da annashuwa.
Slim B, ya ce waka baiwa ce domin kuwa tun da ya taso yake da sha’awar waka, hakan ne ma yasa shi bin wasu hanyoyin da suka dace domin tabbatar da ya cimma burinsa.
Slim B, ya kara da cewa ban da waka, yana harka hadawa tare da tace waka ga masu bukata, sannan yana dauka bidiyo yana kuma kidi, duk a lokaci guda. Kana yana wakokin ingausa ne domin shi ne abin da ake yayi a yanzu.
Yana isar da sakonnin salama da ba da kwarin gwiwa ga matasa, wajen tabbatar da cewar dukkanin mai buri ko bukatar aiwatar da wani abu ya tabbatar ya sa kuzari da jajircewa wajen ganin hakan ya yiwu.
Ya ce daga cikin matsalolin da mawaka ke fuskanta shine wajen tallata wakoki, da ganin cewar sun isa wasu wuraren da mawaki ba zai iya zuwa ba, ya na me cewa manya mawaka a wasu lokutan basa ciccibar kananan mawaka wajen ganin sun kai ga haske.
Your browser doesn’t support HTML5