Ministan Gidaje da Ayyuka da kuma Wutar Lantarki na Najeriya, Alhaji Babatunde Raji Fashola, yace “Yarjejeniyar da mukayi da hukumar bada hasken wutar lantarki ta kasa shine, a bada lokaci nan da shekaru goma kuma in an duba wannan farashi sosai za a ga cewa nan da shekaru biyu daga yanzu farashin na iya saukowa kasa sosai.”
Amma kungiyar Kwadago ta Najeriya tace da sake, shugaban kungiyar Kwadago na kasa kwamared Ayuba Waba, ya fadawa wakilin Muryar Amurka cewa basu yar da ba.
Inda yace zancen a hada kwaya mai daci ma bai tasoba, domin in aka duba duk bayanan da ministan yayi babu bayanin da yake gaskiya ciki, an dai yi wannan kari kuma mutane basa samun wuta amma suna biyan kudin wuta, wannan ba zai yiwu ba inji shugaban kungiyar Kwadago na Najeriya.
Saurari cikakken rahotan.
Your browser doesn’t support HTML5