Matsayar Hukumar Kiyaye Hadurra Ta Kasa Akan Lasisin Tuki

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa wato Federal Road Safety Commission, ta fitara da sanarwar cewa har yanzu bata canza kudin da take amsa wato Naira 6,350 na yin lasisin tukin mot aba, kuma ta kara da cewa kada kowane direba mai neman lasi ya biya abinda ya wuce haka wajan neman lasisin tuki mai wa’adin shekaru uku.

Hukumar ta ce, bata sanar da kara farashin samun lasisin tuki ba, ta kuma kara da cewa ta kara wa’adin shekaru biyar ne akan lasisin mai wa’adin shekaru uku wanda farashinsa Naira 10,350, ne domin ba masu motoci zabi.

Babban kwamandan hukumar kiyaye hadurra Mr Boboye Oyeyemi ne ya yi nuni da hakan yayin da yake Magana a wani taro da aka gudanar a jihar Legas, kuma ya gargadi masu motoci kada su nemi lasisi ta bayan fage.

Mujallar Daily Post ta wallafa cewa shugaban ya bayyana neman lasisi ta bayan fage ko jabun lasisi a matsayin babban laifi.

Daga karshe Mr Oyeyemi ya bayyana cewa jami’an hukumar bazasu ragawa duk direban da suka kama da laifin mugun gudu fiye da yadda doka ta tanada, lamarin da ke haddasa karuwar yawan hadurra a kasar.