Arewacin Nijeriya na fama da matsalolin rashin baiwa mawaka muhimmanci, kamar yadda ake bawa mawaka a sauran sassan kasar nan ta fannin taimaka musu daga bangaren gwamnati da sauran kamfanoni masu zaman kansu, inji ta bakin mawaki Abdulhassan Abdulkaram Arewa Young Fish.
Na bar waka duba da yadda ake nuna kabilanci da bambanci ga sauran mawakan, ba kamar wasu a sassan Nijeriya ba, ko da ya fara waka matsalolin addini da kabilanci kan dakatar da yanayin wakar sa.
Mutanen arewa kamar yadda yake cewa sun taimaka wajen tauye sana’ar, na rashin basu goyon baya, hakan ce ta sa a yanzu ya daina waka domin yana zuba jari, kuma baya samun ribar abinda yake so, sannan ga sa idon alumma da ke hana ruwa gudu.
Young Fish dai a yanzu ya daina waka domin baisamu goyon baya da yake muradi ba, amma fa a ta bakinsa har kawo yanzu yana nan yana marawa mawaka masu tasowa domin cimma burinkan su na daukaka da girmamawa.
Your browser doesn’t support HTML5