Yayin da sababbin gwamnonin da aka rantsar ke fara kama bakin aikin su, jihar Adamawa kuwa da alamun za’a fara ne da din bin matsalolin da aka gada, wanda suka hada da dinbin basusussuka da batun Boko Haram sai kuma na yajin aikin da ma’aikata da suka shafe wata da watanni suna yi.
Wannan ma na zuwa yayin da ayau litinin tsohon gwamnan jihar da aka tsige Murtala Nyako zai koma Adamawa, bayan gudun hijiran da yayi a kasar waje.
Kwamarad Baba Gurin Abbo da ke zama shugaban hadakar kungiyar ma’aikatan kotuna ta Najeriya reshen jihar Adamawa ya bayyana bukatarsu ga sabuwar gwamnatin jihar inda yace, “mun shafe wata biyar muna yajin aiki, wata biyar ya janyo mutane duk sun galabaita.”
Itama rundunar ‘yan sandar jihar ta bayyana damuwar ta ne game da matsalolin da suke fuskanta sadiyyar yajin aiki na ma’aikatan kotuna.
To amma kawo yanzu ba’a san da ko wanne bangare ne na ‘yan malisar dokokin jihar sabuwar gwamnatinzatayi amfani da su ba, tsakanin ‘yan bangaren Amadu Umaru Fintiri da kuma ‘yan ta lauyan majalisa na Jerry Kundisi dake zama a agidan gwamanti.
Saurari cikakken rahotan.
Your browser doesn’t support HTML5