Wasu daga cikin hanyoyin dai sun hada da kiran wayar mutun tare da shaida masa cewar daga bankin da yake ajiya ake kiransa, wato customer care, - alhali kuwa 'yan danfara ne. Sau da yawa dai sukan aiko da wasu lambobi da suke neman ka gaya masu lambobin, da zarar mutum ya fada tarkonsu, sai su wawure kudaden ajiyar mutane ba tare da bata wani lokaci ba.
Sau da yawa dai sukan bugo wayar ne bayan an tashi aiki ranar Juma'a zuwa Asabar da Lahadi, wato ranakun da suka san bankuna basa aiki, balle wanda aka danfara ya garzaya banki domin neman ceto.
Ko wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin ya taba fuskantar irin wadannan 'yan danfarar da suka buga ma shi waya har sau 23 duk kuwa da cewa wayarsa ta nuna 'yan danfara ne.
Ko a watan Satumba sai da jami'an hukumar FBI suka kama wasu 'yan asalin Najeriya dake zaune a Amurka da suka danfari wasu 'yan Amurka fiye da 100 dala miliyan 117.
Saurari rahoton Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5