A jihohin biyu masu ababen hawa sukan shafe awanni da dama ko kuma su kwana suna jiran tsammani cewa zasu samu man su saya.
Sau tari saboda cikonson mutane da rashin tabbas jama'a sukan hasala har su ba hammata iska tare da hatsaniya.
Masu ababen hawa suna zargin dillalai da masu dakon mai a matsayin umalubaisan matsalar da suke fuskanta. Sun zargi dillalan da kin sayar da man a farashen gwamnati duk da cewa an biyasu tallafi.
Masu korafin suna ganin zagon kasa suke son su yiwa shugaban kasa. Sun yi addu'ar fatan Allah ya bashi nasara bisa ga ayyukan da ya sa gabansa da zai yiwa kasar. Fatansu shi ne su samu mai da rahusa domin daukan fasinjojin idan kuma basu samu ba to aikinsu ya zama banza domin babu riba, ciyar da iyansu kuma zai zama da wahala.
Duk da matsalar a gidajen mai a bayan gari 'yan bumburutu na cin karensu ba babbaka. Suna sayar da mai a bakin hanya. Ya wadata a wurinsu amma a bisa nasu farashen suke sayarwa.
Sakataren hadakar kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya reshen Taraba da Adamawa ya mayar da martani akan zargin da aka yiwa kungiyarsu. Abdulmalik Bello yace masu shigo da man su ne suke karbar tallafi daga gwamnati su kuma zagaya su sayar masu da mai din akan farashin da suka kayyade ma kansu, wato suna da tallafi kashi biyu ke nan. Ga na gwamnati ga farashen da suka sayar masu.
Shi ma sashen dake kula da albarkatun man fetur ta bakin kakainsa Akim Musa yace kullum suna hukumta gidajen man da suka sabawa doka.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5