Duk da dage zaben da aka yi a makon da ya gabata hakan ba zai jefa wasu daga cikin matasa canza ra’ayoyinsu ba ta hanyar karba na goro ko kwayoyi ba, domin gudanar da bangar siyasa ko ta da hargitsi a lokacin kada kuri’u ba.
Matashi Ibrahim Dan Baba Zage, mai bawa shugaban karamar hukumar birni shawara akan harkokin matasa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA a Kano.
Ya ce karba na goro ko kwaya ba abinda matasa suka sa a gaban su ba Kenan illa, a yanzu matasa sun farga su na kuma kokarin kauracewa bangar siyasa, a cewarsa matasa sun san cewar ‘yancinsu ya fi karbar abinda bai taka kara ya karya ba.
Ibrahim ya cemaimakon haka kokarin matasa bai wuce su gina kansu wajen samun karbuwa a cikin al;ummar su domin ganin cewar da zarar an kafa wannan sabuwar mulki lallai ragamar mulki ya kamata a koma ga matasa.
A don haka kokarin matasa yanzu shine tabbatar da matasa sun samu shiga cikin harkar demokradiya da wayar da kan yan uwansu matasa illar shaye-shayen kwayoyi da kuma daina biye wa iyayen gida wajen taimaka musu dare kujerar mulki.
Ya kara da cewar babbar matsala siyasar matasa bai wuce rashin isashun kudade a hannun matasa da zai basu damar karbar mulki kamar yadda matasa ke kawo cigaba a harkokin siyasa a kasashen da suka cigaba a duniya.
Your browser doesn’t support HTML5