Matashiyar, wacce ba a bayyana sunanta ba, ta isa wurin ne inda ta fara buga kofar ofishin na ‘yansanda da ke kusa da birnin Los Angeles, a yammacin Lahadi.
Yayin da jami’an suka je bude kofa, matashiyar ta yi nasarar kwace wata bindiga daga daya daga cikinsu.
Ofishin ‘yansanda ta gundumar Los Angeles ta ce a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa "matashiyar ta kutsa cikin harabar ofishin ne inda ta kai hannun ta kwato bindigar mataimakin sufeton."
Sanarwar ta ci gaba da cewa, "an yi taho-mu-gama tsakanin mataimakan sufeton da matashiyar da ke dauke da bindigar mataimakin."
"A lokacin gwagwarmaya, matashiyar ta raunata kanta da bindiga."
Matashiyar ta mutu nan take a cewar ma’aikatan lafiya da suka isa wurin.
Jami'an da ke bincike sun ce sun fara binciken ne biyo bayan kiran iyayenta da suka rene ta suka kira don ba da rahoton cewa matashiyar na fama da matsalar tabin hankali.
"Yansanda sun mayar da martani a lokacin; sai dai, matashiyar ta riga ta tafi da ƙafa kafin su iso," in ji sanarwar.
"Ba a san inda matashiyar ta nufa ba a lokacin da aka yi kiran."
Tashin hankali tsakanin ‘yan sanda da jama’a ba bakon abu ba ne a kasar.
Wani rahoto da jaridar Washington Post ta fitar ya nuna cewa sama da mutane 1,100 ne 'yan sanda suka harbe a fadin kasar a cikin watanni 12 da suka gabata.