Matashiya Mai Hada Karatu Da Sanna'ar Hannu

Matashiya Zahra'u Abdulrahman Muhammad ta ce ta fara sana’a dinki ne sakamakon sana’ar da ta taso ta ga mahaifiyarta na yi. Wanna shi ya sa ta fara dinki a cikin gida a lokutan da ba ta zuwa makaranta.

Ta faro wannan sana’a ne shekaru uku da suka gabata inda ta koyi dinki a wajen kawar mahaifiyar ta, kuma ita ma mahaifiyar ta, ta koya mata yadda ake yanka ta hanyar zane da sauran dabaru na dinki.

Ta ce ta kan dauki samfarin dinki a wajen kawayenta, ko a jikin mutune. Da zarar ta ga dinki, lallai zata iya dinkawa kuma tana iya dinka makamanci wanda aka kawo mata. Ta kan yi wannan sana’a ta ta ne a lokacin da babu makaranta. A cewar ta, ta ajeye kowanne a fannin sa, ma’ana, tana karatunta kuma tana sana’ar hannu.

Akan yi wa tailoli ikrarin basa cika alkawari, a na ta bangaren, takan kamanta ciki alkawari ta hanyar karbar aikin da za ta iya kamala a lokacin da ta deba, sannan daga cikin kalubalen da ta ke fuskanta, sun hada da rashin biyan kudin dinki a ta bakinta.

Mafi yawan lokuta sai mutum ya kawo dinki da cewar suna son dinkin gaggauwa, amma da zarar an kamala masu, sai biyan kudi ya ci tura, wannan na daga cikin abinda ke tauye ma ta sana’a.

Your browser doesn’t support HTML5

Matashiya Mai Hada Karatu Da Sanna'ar Hannu