Matashin Da Ke Sana'ar Waka Da Kiwon Dabbobi

Abdulrahin Zero

Abdulrahin Zero

Abdulrahim Zero makadi, kuma mawaki a masana’antar Kannywood. Ya ce bai cika fuskantar matsalar satar fasaha ba sakamakon mafi yawan lokuta wakokin da yake yi, domin sai an biya tukunna ya ke yin su.

Ya ce sha’awa ce ta sa ya fara waka kuma yana wakar hip-hop da wakokin nananye, ko na fina-finai, sannan ya ce akwai tsare-tsaren da ya daukar wa kansa na kaucewa satar fasaha, domin wakokinsa na sayarwa ne.

Ya kara cewa ban da waka yana da sana’ar da ya dogara da ita, wato kasancewarsa bafulatani, yana kiwo domin taimakawa kansa wajen samun kudaden shiga.

Zero ya ce, ya fuskanci matsala daga wajen mahaifinsa domin ba ya son wakar da yake yi, ya fi masa burin ya je makaranta, a don haka ne a yanzu wakokinsa ba sa wuce faifan murya kadai, har ya kawo yanzu bai yi faifan bidiyo ba.

Ga cikakken rahoton hirarsu da wakiliyar Murayr Amurka Baraka Bashir.

Your browser doesn’t support HTML5

Matashin Da Ke Sana'ar Waka Da Kiwon Dabbobi