Matasa fiyeda 200 ne suka fito daga jihohi takwas na Nijar, hade da matasan kasashen Mali da Burkina Faso suka kammala wani taro a birnin Agadez dake arewacin Jamhuriyar Nijar inda suka tattauna a kan matsalolin da ke addabarsu domin samun mafita.
Matasan sun kuma tattauna kan hanyoyin samun mafita kan wadannan kalubale dake gabansu wadanda ke kawo musu cikas ga cigaban rayuwarsu.
Birnin Agadas ne ya karbi bakunci taron matasan inda suka shafe kwanaki biyar suna sada zumunci da samar da hadin kai a tsakaninsu.
Mahamadu Umaru, wanda matashi ne da ya fito daga jihar Maradi, yace wajibi ne matasan Afirka su tashi tsaye domin samarwa kansu ingantacciyar rayuwa.
Shi kuma Sidi Mohamed wanda shine Shugaban Majalisar Matasan Kasar Nijar, kira yayi ga matasan da su hada kansu domin samar da cigaba ga kasashensu.
Daga karshen taron, matasan sun fitar da wani kundi wanda a cikinsa akwai shawarwarin da zasu gabatar ma hukumomin kasashen wanda suke ganin idan anyi anfani dasu za’a iya magance matsalolin da matasan ke cin karo dasu a kasashen dake yankin Sahel.