Matasan Nijar Sun Yi Taron Neman Zaman Lafiya Da Hadin Kai

Lokacin bikin komawar Nijar Kungiyar ITIE

Lura da yadda dalilan siyasa ke zama wata hanyar haddasa rarrabuwar kawunan jama’a a yau a wannan nahiya, ya sa kungiyar Les Nigeriens sont des cousins daukar matakan kaucewa fadawa irin wannan tarko.

Kungiyar matasa masu fafutukar kawar da bambancin kabilanci daga kawunan jama’ar Jamhuriyar Nijar ta shirya wani taron saukar Alkur’ani mai girma a yau Lahadi 2 ga watan Yuni da nufin rokarwa kasa da makwabtanta kubuta daga matsalolin ta’addancin da suka addabe su.

An gudanar da karatun ne a farfajiyar makarantar faramarin Boukoki ta 4 da ke Yamai inda dimbin jama’a ta hallara a wannan domin karatun Alkur’ani mai girma wanda kungiyar matasa masu fafutukar kawar da bambancin kabila da ake kira Les Nigeriens sont des Cousins ta shirya don neman zaman lafiya a kasa.

Kungiyar wacce ke kunshe da matasa maza da mata na ciki da wajen Nijar masu amfani da kafafen zamani na da burin mayar da hankali akan al’adun gargajiya don karfafa dankon zumunci a tsakanin al’umomi in ji jagorar wannan tafiya Haoua coulibaly.

Lura da yadda dalilan siyasa ke zama wata hanyar haddasa rarrabuwar kawunan jama’a a yau a wannan nahiya, ya sa kungiyar Les Nigeriens sont des cousins daukar matakan kaucewa fadawa irin wannan tarko.

Wannan shi ne karon farko da matasa ke kafa kungiyar yaki da bambancin kabilanci a nan Nijar matakin da tuni ya samu karbuwa daga mahukuntan wannan kasa saboda gamsuwa da sakwannin hadin kai da mambobin kungiyar ke aikawa al’uma ta hanyar kafafen sada zumunta wadanda a yau ke zama wani babban dandalin zazzafar mahawara.

Saurari cikakken rahoton Sule Mumuni Barma daga Yamai:

Your browser doesn’t support HTML5

Matasan Nijar Sun Yi Taron Zaman Lafiya Da Hadin Kai - 2'34"