Kungiyoyin matasan Krista a Jamhuriyar Nijar, sun gudanar da babban taronsu na shekara-shekara, taron da ke nazari kan abubuwan da suka shafi matasa.
Wannan karon a taron, sun maida hankali kan rawar da matasa Krista za su taka a ci gaban kasa, da kuma yadda za su kauce wa shiga kungiyoyin ta'addanci.
A bana, matasan sun kuma maida hankali kan yadda za su zama masu kishin kasa, da rawar da za su taka a gina kasa, tare da yadda za su kauce wa afkawa ta'addanci.
A cewar Adamu Mai Daji, shugaban kungiyar matasan Krista a Nijar, sun dauki wannan mataki ne, tare da la'akkari da suka yi a halin da ake ciki, na yadda ake amfani da matasa a cikin kungiyoyin ta'addanci, ko tashin hankali na addini, ko siyasa
Hakan ne ya kawo, su wayar da kan matasa, game da illar hulda da wadannan kungiyoyi, ko maida kankanuwar magana ta koma fitina.
Ya kuma yi kira ga matasan, da su zage dantse wajen sanin dokokin kasa, da aiki da su.
Shi ma Reverand Kannai Garba na Maradi, ya ce gudunmawar su ta iyaye, ita ce su koyar da su, da fahimtar da matasan yadda za su yi mu'amala da sauran addinai.
Ga cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Tamar Abari.
Your browser doesn’t support HTML5