Matasan Karamar Hukumar Miango A Jihar Filato Na Neman Hukunci

Matasan yankin Miango dake karamar hukumar Bassa a jihar Filato, suna kira ga hukumomi da su kara kaimi wajen bankado wadanda suka yi kisan gilla ga wasu mutane 29 a wata makaranta, shekaru 2 da suka gabata.

Matasan suna sanye da bakaken tufafi kana sun taru akan hanyar zuwa sakatariyar gwamnatin jihar Filato, suna masu cewar sun fito ne don su nuna juyayi kan kisan ‘yan uwansu a kauyen Nkidongrwo, suna kuma jan hankalin hukumomi da su kara kaimi wajen gano wadanda suka aikata kisan.

A bayanin sa ga muryar Amurka, shugaban matasan na Miango, David Shinge, yace tun bayan abkuwar lamarin basu samu wani bayani daga hukumomi ba, don haka suna neman gaskiya ne, domin zaman lafiya.

Ita kuma Esther Yakubu Chai, tace a yanzu an samu saukin tashin hankali a yankin nasu, amma suna neman taimako daga gwamnati, domin a kara kokarin kawo karshen kashe-kashen rayuka.

Kwamishinan yada labaran jihar Filato, Dan Manjang yace gwamnati na iyakar kokarinta wajen samun zaman lafiya a jihar.

Ga rahoton mu cikin sauti wanda Zainab Babaji ta hada muna.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasan Karamar Hukumar Miango A Jihar Filato Na Neman Hukunci