Matasan Birnin Kano Sun Bayyana Shirin Su Na Zabe

Matasa a birnin Kano sun bayyana ra'ayoyin su dangane da irin shirin da suka yi domin yin zabe wanda za a yi a ranar Asabar 16 ga watan nan.

Bashir Abdullahi ya ce tuni ya shirya tsaf domin zaben ranar Asabar mai zuwa, a cewar sa ya yi shirin ne domin zaben cancanta da ci gaban kasa ta hanyar zaben jagoran da zai ba da ilimi, da tabbatar da tsaro, shi ya sa tuni ya adana katin zaben sa yake kuma jiran ranar zabe.

Shi kuma Muhammad Auwal Suleman cewa yayi tuni ya kira mambobin kungiyarsu domin gudanar da zabe cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, tare da jan hankalin mambobin kungiyar ta su ta makaranta akan cewar duk wanda ya kada kuri’ar sa ya koma gida domin sauraron sakamakon zabe, maimakon jira a filin zabe.

Ya kuma kara da jan hankalin matasa akan su fita cikin nutsuwya kuma ya tunatar da su akan kauracewa yaudarar 'yan siyasa domin ta da hargitsi.

Wani matashi Muhammad Alkassim, cewa yayi tuni ya shirya wajen tabbatar da kawo canji na ci gaban kasa da al'umma baki daya. Ya kuma bayyana cewa ya shawarci iyalinsa da 'yan uwansa wajen fita komai rana komai zafi domin zaben cancanta.

Shi kuma Sadi Sharif cewa yayi hukumar zabe ta shirya wajen inganta harkar zabe tare da yawaita tunatar da al'umma, a saboda haka shima ya shirya wajen tabbatar da ya bi dokokin hukumar zabe wato INEC.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasan Birnin Kano Sun Bayyana Shirin Su Na Zabe - 4'31"