A taron manema labarai da kungiyar ta kira ta bayyana cewa, dubban jama’a ne daga kananan hukumomin Barikin Ladi da Riyom ke gudun hijira, lamarin da ya sanya ‘ya’yansu shiga halin ha’ula’i.
Choji Dalyop, shugaban kungiyar matasan Berom ta kasa da kasa ya bayyana cewa, akwai mutane da yawa da rikincin ya tada su daga gidajensu, ya zama da dama basu iya komawa gida suyi noma. Wannan ya jefasu cikin matsananciyar wahala.
Yace sun kira taron manema labaran ne domin gabatar da damuwarsu. Bisa ga cewarsa suna da wurare guda hamsin da hudu da hargitsi yasa al’umar Berom suka kauracewa wuraren, yace wuraren da suke tsugune yanzu haka ya cunkushe ya kasa masu, ya kuma bayyana cewa, gwamnati tana da ‘yanci tasa mutanen su koma wurarensu.
A nashi jawabin, Barrister Dalyop Solomon daya daga cikin ‘ya’yan kungiyar yace suna goyon bayan gwamnatin jihar Plato ta kafa dokar hana kiwo a fili. Ya bayyana cewa, satar shanun da ake yi , ba a ruga ake binsu a sace ba, ana sace su lokacin da aka fita dasu kiwo. Yace abinda zai taimaka wajen kawo karshen satar shanun shine a hana kiwo a fili wanda yake haifar da rikicin tsakanin manoma da makiyaya. Yace suna fargaban kada gwamnati tayi amfani da wuraren mutane da rikicin ya tilasa kaura wajen maida su wuraren kiwo.
Saurari Rahoton Zainab Babaji domin jin bayanin gwamnan jihar Plato Simon Lalong kan wannan batun
Your browser doesn’t support HTML5