Yanzu haka dai dubban ‘yan gudun hijira daga jihar Benue ne suka kwarara zuwa garin Tunga dake cikin karamar hukumar Awe a jihar Nassarawa.
‘Yan gudun hijiran wadanda yawancin su ‘yan kabilar tiv ne da Fulani sukace sun guje wa muhallan su ne domin gudun kar rikicin ya rutsa dasu.
To sai dai wani abu mai daure kai, shine ardon ardodin jihar Nassarawa Ardo Lawan Dono, ya shaidawa wakiliyar sashen Hausa Zainab Babaji cewa, ba makiyaya ko manoman na jihar ta Benue ne suka kawo wannan fadan ba.Yace wannan yasa suke zaune lafiya da junan su.
Sai dai duk lokacin da irin haka ta faru wannan gari na Tunga yakan cika da jamaa domin yana zama tamkar tudun natsira ne.
Shugaban kungiyar raya al’ummar garin na Tunga Alhaji Saidu Mohammad ya bukaci gewamnati dama masu hannu da shuni da su taimaka musu domin ko kudin kungiyar ya kare wajen agajin da suke baiwa wadannan mutanen dake gudun hijira a garin nasu.
Gwamnan jihar ta Nassarawa yace sun kashe kudi har sama da naira miliya 50 domin agazawa wadannan bayin ALLAH kuma ba zasuyi kasa a gwiwa ba.Haka kuma zai tabbatar an inganta matakan tsaro a wannan yankin.
Ga Zainab Babaji da Karin bayani 3:32
Facebook Forum