Matasan Amurka Sun Fi Bukatar Ganawa Ta Text Akan Kai Tsaye

Matasa a kasar Amurka sun fi sha’awar ganawa da abokan su ta hanuar aika sakon gaggawa na “Chart ko text”fiye da yin Magana da abokan nasu a fili ka ta waya.

Sun tabbatar da cewar ai kuwa koda sun hadu a lokutta da yawa basu iya yin wata tattaunawa mai ma’ana kamar yadda zasu yi ta hanyar sadarwar sakon gaggawa.

Sau da yawa zasu haddu amma ganawar su bata karfi da kuma zata haifar da wata tattaunawa mai ma’ana, domin kuwa a duk lokacin da suka hadu wasu abokan su kuma zasu dinga aiko musu da sakonni wanda bazasu iya kyale su batare da sun amsa musu ba.

Wani sabon bincike da wani kamfanin mai suna Common Sense Media, ya gudanar wanda ya tabbatar da cewar fiye da rabin matasa tsakanin shekaru 13 zuwa 17 sun amince cewar kafofin sadarwar zamani na dauke musu hankali matuka, wajen mu’amalarsu ta yau da kullun har ma da ayyukansu.

Su kuwa kashi daya cikin uku cewar sukayi shafukkan yanar gizo na hargitsa musu walwalar su da yanayin baccin su, kimanin matasa 8 cikin 10 kan kasha lokaci mai tsawo a shafukkan yanar gizo, abun bai canza ba tun daga sakamakon binciken da aka wallafar a shekarar 2012.