Shugaban Amurka, Barack Obama, ya umarci matasan Afirka, masu halartar wani shiri da shugaba Obama, ya bullo dashi na karfafawa matasan Afrika gwiwa domin zama shuwagabani na gari dasu tabbatar da cewa sun aiwatar da abubuwan da suka koya domin ciyar da nahiyar Afirka gaba.
Ya furta haka ne a lokaci da yake yiwa matasan wannan shiri jawabi a birnin Washington, yace hakan ya zama wajibi domin nan gaba su zasu jagoranci nahiyar Afirka.
Ya kara da cewa Amurka zata horas da matasa daga Afirka, a fannonin kasuwaci , kimiya da shugabanci, yace domin ya gamsu da sakamakon daya samu akan su daga malaman dake hurda dasu.
Shugaba Obama, yace a mako mai zuwa zai karbi bakuncin shuwagabanin kasashen Afirka, inda zasu tattauna abubuwa da dama da suka hada da batun tsaro, kiwon lafiya, kasuwanci da wutan lantarki.
Shugaban na Amurka, ya kuma yi albishir din cewa a shekaru biyu masu zuwa za’a gudanar da wannan taron a nahiyar Afirka, a kasashen kamar Senegal, Afirka ta kudu, Kenya da kuma Ghana.
Taron da aka fi sanisa da babban taron Washington, yanzu ya zama babban taron Mandela na Washington, kuma daga shekara mai zuwa masu halartan taron zasu zama su dubu daya amaimakon dari biyar.