Matasa Sun Yi Cincirondon Shiga Aikin Soja a Ivory Coast

Wasu matasa ke nan ke goyon bayan Laurent Gbagbo.

Dubban matasan kasar Ivory Coast/Cote d’Ivoire, sun yi cincirindo a birnin Abidjan domin shiga aikin sojin kare shugaban kasar mai ci Laurent Gbagbo, wanda ke ci gaba da yin kunne kasha ga kiraye-kirayen da ake masa cewar ya mika mulki.

Matasan sun fara haduwa ne a ma’aikatar tsaro litinin da safe domin shiga aikin soja a wani mataki amsa kiran Charles Ble Goude, wanda ke shugabantar kungiyar matasan dake goyon bayan Laurent Gbagbo da aka sani da sunan ‘Young Patriots’.Goude, wanda shine Ministan Matasa a Gwamnatin Gbagbo da ake takaddama kanta, yayi kira fa matasan na Ivory Coast da su kokarta kubutar da kasar.

Charles Ble Goude tsohon shugaban dalibai, shima suna shi na cikin jerin wadanda kadarorinsu suka ci karo da takunkumin MDD, da kuma haramcin yin bulaguro tun shekarar dubu biyu da shida, saboda laifin da ya aikata a can baya na tura mutane syu yi tashin hankali.Mr. Laaurent Gbagbo ya kalubalanci matsin lambar da kasa da kasa ke yi masa kan sailallai ya mika mulki fa Alhassan Outtara wanda MDD da kungiyar kasashen Afirka suka amince da shine a matsayin wanda ya sami nasara a zaben shugaban kasar da aka gudanar a cikin watan Nuwamba.