Matasa Musulmi Sun Bada Tsaro a Coci Coci a Bikin Kiristimeti

Wasu yara sun ce bikin ba kamar yadda suka saba gudanar dashi bane a garuruwansu

Yayin da Kiristoci a fadin duniya ke gudanar da bukukuwan Kiristimeti wasu ‘yan gudun hijira sun bukaci Gwamnati ta samarda tsaro a yankunansu domin su koma gidajensu.

A jihar Filato, hidimomin Kiristimeti sun gudanar ne cikin tsauraran matakan tsaro.

A Majami’ar Ikilisiyar ‘yan uwa a Najeriya, wakiliyar murya Amurka Zainab Babaji ta samu tattaunawa da wasu domin jin yadda bikin na bana ke gudanar .

Wasu yara sun ce bikin ba kamar yadda suka saba gudanar dashi bane a garuruwansu.

Wasu iyaye kuwa cewa suka yi sun godewa Allah, amma sun so Allah ya kawo sauki su koma gida domin suna fuskatar matsala.

Shugaban matasa na E.Y.N Imon Sunday, yace har yanzu ba’a samu kwanciyar hankali ba a yankuna ta yadda ‘yan gudun hijira zasu koma ba, amma idan sauki ya samu mutane zasu koma.

A cewar mataimakin Paston Majami’ar, suna amfani da wanna lokaci Kiristimeti, don adduo’in samu tsaro a Najeriya.

Wani abun ban sha’awa shine yadda matasa Musulmi suka baiwa Kiristoci tsaro a Majami’u, yayin gudanar da Sujadar Kiristimetin.

Abdulmumini Aliyu, daya daga cikin wadanda suka bada tsaro a Majami’ar yace saboda hadin kan al’uma yasa suke taimako a tsakanin su da Musulmi da Kiristoci saboda halin da kasar take ciki.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasa Musulmi Sun Bada Tsaro a Coci Coci a Bikin Kiristimeti - 4'56"