Gwamnatin jihar Nasaraw ta ce ta kammala dukkan shirye shirye da kamfanin Dangote, dan kafa masana’antun sukari da shinkafa wanda zai samawa matasa Dubu Talatin ayyukanyi a jihar.
Kwanan nan ne gwamnatin jihar Nasarawa ta rattaba hannu da kamfanin akan wata yarjejeniyar mallakar wani katafaren fili mai fadin kadada dubu dari, da biyan masu filayen dake yankin Tunga diyyar kudaden filayen su da aka amsa dan kafa wannan kamfani na sarrafa sukari da shinkafa.
A zantawa da gwamnan jihar Umaru Tanko Almakura, bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar, ya bayyana cewa jihar wadda aka kirkiro shekaru ashirin da suka gabata, na yunkurin cimma sauran takwarorinta ne wajan bunkasar tattalin arziki.
Daga bangaren matasan jihar kuwa, sunce alasambarka, domin kuwa wannan sabon kamfani zai rage radadin zaman kashe wando da kuma bunkasa tattalin arziki da kuma magance banker siyasa da matasan ke sa kawunansu ciki sakamakon rashin ayyukan yi.
Kimanin kudi Naira Biliyan dari biyu da sittin kamfanin zai yi kashe wajan zuba jari a wannan sabon kamfani.
Domin karin bayani ga rahoton Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5