WASHINGTON D.C —
Ya kamata matasa su daina raina sana’a ko jarin da zasu fara sana’a da shi, domin kuwa da ruwan ciki ake jan na rijiya, kuma da kadan-kadan jari yake zama babba, inji wata matsashiya mai sana’ar hijabi da kayan gumama, Malama Jamila Ahmad Yakasai.
Da take zantawa da wakiliyar DandliVoa, Malama Jamila ta ce takan bude dilar gwanjo ta kayan yara a hannu guda kuma tana dinka hijabai na mata da kananan yara duk a yunkurin zama mai dogaro da kai.
Ta kuma kara da cewa duk kuwa da wannan sana’ar ta bata hana mata neman ilimi ba, kuma babu takurawa a harkokinta na gida misali wajen lura da mai gida da ‘ya’yanta.
Daga karshe Jamila, ta ce tana koyawa matasa yadda ake dinka hijabi ba tare da ta karbi ko kabonsu ba.
Your browser doesn’t support HTML5