Taken taron nasu shi ne inganta jima'i da samarda kiwon lafiya tsakanin matasa 'yan mata.
Kusan duk wadda tayi jawabi a wurin taron ta bayyana irin shirinta ne da ta keyi dake taimakawa al'umma.
Matar shugaban kasar Ghana Dr. Nana Dramani Mahama ta bada haske akan irin rawar da shirinta ke takawa wajen kyautata rayuwar 'yan mata a Ghana.
Ita ma matar shugaban kasar Saliyo Madam Sarah Koroma tace shirinta ya taimaka saboda 'yan matan kasar sun karu da ilimin jima'i kodayake abu ne mai wahala a fito fili ana irin wannan maganar a al'ada irin ta Afirka.
Ita ko matar shugaban kasar Namibia Madam Monica tace shirinta ya kubutar da mata cikin kangin cutar kanjamau domin ta mayar da hankali ne akan matan karkara inda take fadakar dasu akan jima'i.
Matar shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari tace shekara guda ke nan da ta samar da nata shirin mai taken "Muna da Kwarin Gwuiwa Gobe Zata Yi Kayau".
Bayan an kammala taron Muryar Amurka ta yiwa Aisha Buhari wasu tambayoyi. Dangane da ko shirin zai taimaki mata a Najeriya sai tace zai taimakawa mata ta hanyar samun lafiya da hanyar koyon sana'a, da shirin kayyade iyali.
Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5