Matan Karkara Sun Tashi Haikan Don Ayyukan Ci Gaban Al'umma

Bukin auren 'yan mata marayu

A yayinda a yau Laraba 8 ga watan Maris ake bukukuwan ranar mata ta duniya mata a kauyen Kouraye dake jihar Zinder a jamhuriyar Nijer sun dukufa ka’in da na’in a karkashin wani shirin da hukumar WFP da FAO da asusun IFAD suka kaddamar.

Sun yi hakan ne don farfado da kasa a ci gaba da neman hanyoyin samar da wadatar ciyawar dabobi a wannan lokaci da illolin canjin yanayi ke barazana wa sha’anin kiwo.

Nan wasu gomman mata ne muka tarar dauke da felo da diga wasu da fantarya a wani makekenn fili mai hako suna gina ramunan da za a yi amfani da su don bizne irin ciyawar dabobi da nufin farfado da kasar noma da kiwo shirin da hukumar samarda abinci ta duniya wato PAM kokuma WFP ta kaddamar domin tunkarar kalubalen da ake fusknata a fannin cimakar dabobi da ta mutane. Malama Adama Sariou ta bayyana alfanon wannan aiki.

Mita 150 zuwa 200 daga wannan hako wani makeken fili ne lullube da ciyawar dabobi wanda ainahinsa hako ne da aka yi nasarar ceyowa daga yanayin zayzayar da ya fada shekara da shekaru sanadiyyar illolin canjin yanayi. Matan kauyen Kouraye dake da’irar mazamni sun taka rawa wajen neman mafita. Malama Adama Sariou ba ta manta da yanayin filin ba.

A kauyen Dan Gueza dake karamar hukumar Gafatin Jihar Zinder mata sun dukufa wajen kiwon dabobi. Mun iske jagororinwadanan mata abin misali a filin da hukumar PAM ta dauki nauyin dasa itace don yaki da kwararowar hamada sannan an watsa irin ciyawa domin karawa wadanan mata azamar ci gaba da kiwo. Batoula Issa it ace mai magana da yawun mata makiyaya na karkarar Dan Gueza..

Sama da heka 200 na kiwo ne WHO da FAO IFAD suka dauki nauyin farfadowa domin samar da ciyawar dabobi sannan da wasu hekoki sama da 500 da aka ware domin ci gaban ayyukan mata manoma a karamar hukumar Gafati.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

GUDUNMOWAR MATA A AYUKAN CI GABAN AL UMMA.MP3